A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, ana gabatar muku da jerin bahasin Mahdawiyya mai taken "Zuwa Ga Al'umma Mai Manufa", da nufin yada koyarwa da ilimomin da suka shafi Imamin Zamani (A.S).
An fadi maganganu da dama game da ayyuka da nauyin da ke wuyan masu jiran bayyanar Imam Mahdi (A.F); amma a takaice, ana iya raba ayyukan mutane a wannan lokaci zuwa gida biyu:
Ayyukan Bai-Ɗaya
Wannan rukuni na ayyuka, an ambace su ne a cikin maganganun Ma'asumai (A.S) a matsayin wajiban lokacin gaibar Imam; sai dai ba su takaita da wannan lokacin kadai ba, a'a, ya zama dole a aiwatar da su a kowane lokaci. Watakila ambatonsu a matsayin ayyukan lokacin gaiba ya kasance ne domin jaddadawa.
Wasu daga cikin wadannan ayyuka sun hada da:
1. Sanin Imamin Kowane Lokaci
Daga cikin ayyukan da aka jaddada tare da yin umarni a kansu a kowane lokaci — musamman a lokacin gaiba — ga mabiya koyarwar Musulunci, shi ne neman ilimi da sanin Imamin wannan lokacin.
Imam Sadiƙ (A.S) ya ce:
«إِعْرِفْ إِمَامَکَ فَإِنَّکَ إِذَا عَرَفْتَ لَمْ یَضُرَّکَ تَقَدَّمَ هَذَا الْأَمْرُ أَوْ تَأَخَّرَ.»)
"Ka san Imaminka, domin idan ka san Imaminka, gabatowa ko jinkirin wannan al'amari (bayyanarsa) ba zai cutar da kai ba." (Al-Kafi, Juzu'i na 1, shafi na 371
Babu shakka, sanin Imam ba ya rabuwa da sanin Allah Maɗaukakin Sarki; sai dai yana daya daga cikin sassan saninsa. Kamar yadda muke cewa a cikin addu'ar neman sani (Du'a'ul Ma'arifa) ga Allah Maɗaukakin Sarki:
«اللَّهُمَّ عَرِّفْنِی نَفْسَکَ فَإِنَّکَ إِنْ لَمْ تُعَرِّفْنِی نَفْسَکَ لَمْ أَعْرِفْ نَبِیکَ اللَّهُمَّ عَرِّفْنِی رَسُولَکَ فَإِنَّکَ إِنْ لَمْ تُعَرِّفْنِی رَسُولَکَ لَمْ أَعْرِفْ حجّتکَ اللَّهُمَّ عَرِّفْنِی حجّتکَ فَإِنَّکَ إِنْ لَمْ تُعَرِّفْنِی حجّتکَ ضَلَلْتُ عَنْ دِینِی.»
"Ya Allah! Ka sanar da ni kanka, domin idan ba ka sanar da ni kanka ba, ba zan san Annabinka ba. Ya Allah! Ka sanar da ni Manzonka, domin idan ba ka sanar da ni Manzonka ba, ba zan san Hujjarka ba. Ya Allah! Ka sanar da ni Hujjarka, domin idan ba ka sanar da ni Hujjarka ba, zan bata daga addinina." (Al-Kafi, Juzu'i na 1, shafi na 342)
A bayyane yake daga riwayoyin Ma'asumai (A.S) cewa dukkan falaloli da dabi'un kwarai a cikin bautar Allah Maɗaukakin Sarki suna komawa ne ga samun sanin Imam (A.S) da kuma riko da shi.
2. Dawwama a Kan Son Ahlul-Bait (A.S)
Daya daga cikin muhimman ayyukanmu a kowane zamani shi ne nuna soyayya ga Ahlul Baitin Annabi (S.A.W.A) a matsayinsu na masoyan Allah. A lokacin gaiba Shugaba Ma'asumi na karshe, saboda gaibar da Imam ya yi, akwai abubuwa da dama da za su iya nesanta mutum da wannan muhimman aiki; shi ya sa aka yi umarni a cikin riwayoyi da mu kasance masu dorewa a kan son wadannan hasakai masu tsarki.
Kada mu manta cewa wannan soyayya umarni ne na Ubangiji Maɗaukakin Sarki. Shekaru da dama kafin ya fara rayuwar duniya, mutane masu tsarki sun nuna masa soyayya. Manzo mai daraja (S.A.W.A), mafificin Annabawa kuma manzon karshe, sa'ilin da yake magana game da wasiyinsa na karshe, ya yi amfani da kalmomi mafi girma na soyayya da girmamawa, wato: «بِأَبِی وَ أُمِّی; Mahaifina da mahaifiyata su zama fansarka», inda yake cewa:
«بِأَبِی وَ أُمِّی سَمِیی وَ شَبِیهِی وَ شَبِیهُ مُوسَی بْنِ عِمْرَانَ عَلَیهِ جُیوبُ النُّور... .»
"Mahaifina da mahaifiyata su zama fansar sa! Shi mai suna iri daya da nawa ne, kuma mai kama da ni ne, kuma mai kama da Musa dan Imran ne, wanda haske ya kewaye shi..." (Kifayatul Athar, shafi na 156)
Haka kuma, lokacin da Ali dan Abi Talib (A.S) ya kalli zamanin Imami na karshe, sai ya ce:
«فَانْظُرُوا أَهْلَ بَیتِ نَبِیکُمْ فَإِنْ لَبَدُوا فَالْبُدُوا، وَ إِنِ اسْتَنْصَرُوکُمْ فَانْصُرُوهُمْ، فَلَیفَرِّجَنَّ اللَّه [الْفِتْنَةَ] بِرَجُلٍ مِنَّا أَهْلَ الْبَیتِ. بِأَبِی ابْنُ خِیرَةِ الْإِمَاءِ.»
"Ku kalli mutanen gidan Annabinku; idan suka yi shiru suka zauna a gidajensu, ku ma ku yi shiru ku tsaya. Idan kuma suka nemi taimakonku, to ku gaggauta taimaka musu, domin lallai Allah Maɗaukakin Sarki zai kawo mafita (daga fitina) ta hannun wani mutum daga cikinmu Ahlul Bait. Mahaifina ya zama fansar sa! Shi dan mafi alkhairin kuyanga ne." (Biharul Anwar, Juzu'i na 34, shafi na 118)
Khallad dan Saffar ya ce: An tambayi Imam Sadiƙ (A.S): "Shin an haifi Al-Qa'im?" Sai Imam ya amsa da cewa:
«لَا وَ لَوْ أَدْرَکْتُهُ لَخَدَمْتُهُ أَیامَ حَیاتِی.»
"A'a; amma idan na riske shi, da na kasance mai yi masa hidima a kwanakin rayuwata." (Biharul Anwar, Juzu'i na 51, shafi na 148)
A cikin wata riwayar kuma, Imam Baƙir (A.S) ya ce:
«أَمَا إِنِّی لَوْ أَدْرَکْتُ ذَلِکَ لَأَبْقَیتُ نَفْسِی لِصَاحِبِ هَذَا الْأَمْر.»
"Lallai idan na riski wannan ranar, da na karar da rayuwata domin mai wannan al'amari." (Biharul Anwar, Juzu'i na 52, shafi na 243)
Bisa la'akari da wadannan riwayoyi da aka ambata, babu shakka cewa son Ahlul Bait (A.S) — musamman Hujjar Allah ta karshe — a lokacin gaiba, aiki ne mai matukar muhimmanci da kima.
3. Kula da Tsoron Allah (Taƙawa)
Tsoron Allah (takawa) ya zama dole a kowane lokaci; amma a lokacin gaiba, saboda kebantattun yanayi, muhimmancinsa ya fi girma; domin a wannan lokaci, abubuwa da dama suna haduwa don janye mutane zuwa ga bacewa da bata.
Imam Sadik (A.S) ya ce:
«إِنَّ لِصَاحِبِ هَذَا اَلْأَمْرِ غَیْبَةً فَلْیَتَّقِ اَللَّهَ عَبْدٌ وَ لْیَتَمَسَّکْ بِدِینِهِ.»
"Lallai mai wannan al'amari zai yi gaiba; saboda haka bawan Allah ya ji tsoron Allah, kuma ya yi riko da addininsa." (Kamaluddin, Juzu'i na 2, shafi na 343)
4. Yin Biyayya Ga Umarnin Imamai (A.S)
Tunda dukkan Imamai (A.S) haske ne guda daya, umarni da kalamansu duka suna fuskantar manufa guda ce; saboda haka, yi wa kowannensu biyayya tamkar yi wa duka ne biyayya. A lokacin da daya daga cikinsu ba ya nan, umarnin sauran shi ne fitilar shiriya.
Yunus dan Abdul-Rahman ya ce: "Na shiga wurin Musa dan Ja'afar (A.S) sai na ce masa: "Ya dan Manzon Allah! Shin kai ne Al-Qa'im bil-Haqq (Mai tsayuwa da gaskiya)?" Sai ya ce:
«أَنَا الْقَائِمُ بِالْحَقِّ وَ لَکِنَّ الْقَائِمَ الَّذِی یُطَهِّرُ الْأَرْضَ مِنْ أَعْدَاءِ اللَّهِ عَزَّ وَ جَلَّ وَ یَمْلَؤُهَا عَدْلًا کَمَا مُلِئَتْ جَوْراً وَ ظُلْماً هُوَ الْخَامِسُ مِنْ وُلْدِی لَهُ غَیْبَةٌ یَطُولُ أَمَدُهَا خَوْفاً عَلَی نَفْسِهِ یَرْتَدُّ فِیهَا أَقْوَامٌ وَ یَثْبُتُ فِیهَا آخَرُونَ ثُمَّ قَالَ ع طُوبَی لِشِیعَتِنَا الْمُتَمَسِّکِینَ بِحَبْلِنَا فِی غَیْبَةِ قَائِمِنَا الثَّابِتِینَ عَلَی مُوَالاتِنَا وَ الْبَرَاءَةِ مِنْ أَعْدَائِنَا أُولَئِکَ مِنَّا وَ نَحْنُ مِنْهُمْ قَدْ رَضُوا بِنَا أَئِمَّةً وَ رَضِینَا بِهِمْ شِیعَةً فَطُوبَی لَهُمْ ثُمَّ طُوبَی لَهُمْ وَ هُمْ وَ اللَّهِ مَعَنَا فِی دَرَجَاتِنَا یَوْمَ الْقِیَامَةِ.»
"Ni mai tsayuwa ne da gaskiya; amma Al-Qa'im din da zai tsarkake kasa daga makiyan Allah Mabuwayi da Daukaka, kuma ya cika ta da adalci kamar yadda aka cika ta da zalunci da danniya, shi ne na biyar daga cikin 'ya'yana. Yana da wata doguwar gaba saboda tsoron ransa, wanda a cikinta wasu mutane za su fita daga addini (su yi rida) yayin da wasu kuma za su tabbata da gaskiya." Sannan ya ce (A.S): "Sa'ada da bushara ta tabbata ga shi'armu wadanda suke riko da igiyarmu a lokacin gaibar Al-Qa'im dinmu, wadanda suke tsayayyu a kan sonmu da barranta (nesanta) daga makiyanmu; wadannan daga gare mu suke, mu kuma daga gare su muke. Sun yarda da mu a matsayin Imamai, mu kuma mun yarda da su a matsayin 'yan Shi'a. Saboda haka, sa'ada ta tabbata a gare su, sannan sa'ada ta tabbata a gare su. Wallahi, suna tare da mu a cikin darajojinmu ranar kiyama." (Kamaluddin wa Tamamun Ni'mah, Juzu'i na 2, shafi na 361)
Wannan tattaunawa za ta ci gaba
An ɗauko daga littafin "Darsnameh Mahdaviyyat; Wallafar Khodamurad Salimiyan", tare da ɗan gyara kadan
Ra'ayinka